Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta nuna damuwa kan jinkirin naɗa sabon shugaban jami’ar Northwest dake Kano

YUMSUK Northwest University Kano 750x430

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU), reshen jami’ar Northwest dake Kano, ta nuna matuƙar damuwa game da jinkirin da ake samu wajen naɗawa da tabbatar da sabon shugaban jami’ar.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Litinin, wadda shugabar reshen kungiyar, Comrade Mansur Sa’id, da sakataren ta, Comrade Yusuf Ahmad Gwarzo, suka sanya hannu, kungiyar ta bayyana cewa wannan jinkiri na iya janyo rashin daidaito da rikice-rikicen gudanarwa a cikin jami’ar.

Kungiyar ta bayyana cewa wa’adin tsohon shugaban jami’ar ya ƙare ne a ranar 15 ga Oktoba, 2025, inda mataimakin shugaban jami’a mai kula da harkokin karatu ya karɓi ragamar mulki na wucin gadi, duk da cewa dokar kafa jami’ar Northwest ta shekarar 2012 (wanda aka gyara) bata bayar da damar hakan ba.

ASUU ta tunatar da cewa bisa tanadin sashe na 9(2) na dokar jami’ar, ya wajaba ne majalisar gudanarwa ta naɗa sabon shugaban jami’a bayan samun tabbaci daga mai kula da jami’ar.

Ta kuma bayyana cewa an tsara tsarin naɗin cikin doka, wanda ya haɗa da ayyana kujerar a buɗe, kafa kwamiti na bincike, da kwamiti na zaɓe, sannan a tura sunan wanda aka zaɓa zuwa majalisar domin tabbatarwa.

Kungiyar ta bayyana cewa ta sanya ido sosai kan tsarin, kuma ta tabbatar da cewa majalisar gudanarwa ta gama aikin da ya shafi zaɓe, inda ta gudanar da taro na musamman a ranar 2 ga Oktoba, 2025, domin yanke shawara game da wanda za a naɗa.

Sai dai kungiyar ta nuna damuwa kan yadda majalisar ta gaza sanar da sakamakon hukuncinta ga jami’ar da kuma tura sunan wanda aka zaɓa zuwa ga mai kula da jami’ar domin tabbatarwa.

ASUU ta yi gargadin cewa wannan jinkiri na iya zama karya doka, don haka ta bukaci a dauki matakin gaggawa wajen kammala aikin.

Kungiyar ta nemi a tabbatar da gaskiya, bin doka, da kuma guje wa katsalandan daga duk masu ruwa da tsaki cikin tsarin naɗin.

Kungiyar ASUU ta kuma jaddada cewa jinkirin na iya janyo rashin kwanciyar hankali da tabarbarewar gudanarwa, wanda zai iya yin tasiri ga harkokin mulki, tsare-tsare da kuma ci gaban karatu a jami’ar.

Ta tabbatar da aniyarta wajen kare mutuncin tsarin jami’o’i da tabbatar da bin doka a dukkan al’amuran gudanarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here