Kungiyar ASUU Ta Sake Zaben Farfesa Emmanuel Osodoke a Matsayin Sabon Shugaba

ASUU leader
ASUU leader

Mambobin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), da safiyar ranar Litinin sun sake zaɓar Farfesa Emmanuel Osodeke, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar wanda zai sake jan ragamarta na wasu shekara biyu masu zuwa, Osodoke ya lashe zaɓen ne ba tare da wani abokin hamayya ba.

Bayan Farfesa Osodoke wanda ya fito daga jami’ar Michael Okpara University of Agriculture, Umudike, jihar Abia, mambobon ƙungiyar sun sake zaɓar Chris Piwuna, na kwalejin lafiya a jami’ar Jos, a matsayin mataimakin shugaba.

An sake zaɓar shugabannin ne a lokacin taron deliget ɗin ƙungiyar na ƙasa karo na 22, wanda aka gudanar a jami’ar Jos, a tsakanin ranakun 19 da 21 ga watan Mayun.

Sauran shugabannin ƙungiyar na ƙasa da aka sake zaɓa a wajen taron sun haɗa da, Farfesa Siji Sowande (Ma’aji), Farfesa Ade Adejumo (sakataren kuɗi), Dr Austen Sado (sakataren zuba jari) Dr Adamu Babayo (mai binciken kuɗi) da Dr Aisha Bawa wacce ta maye gurbin Dr Stella-Maris Okey a kujerar sakataren walwala.

Osodeke wanda ya bayyana taron a matsayin wanda ya gudana cikin nasara.

A kalamansa: “Mun kammala taron deliget ɗin mu na ƙasa a birnin Jos. Muna kan hanyar komawa birnin tarayya Abuja. Za mu fitar da sanarwa kan taron da sake zaɓe na da aka yi da sauran shugabannin ƙungiyar na ƙasa, idan mu ka koma ofishin mu. Nagode.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here