Kotu ta tsare mutum 10 bisa zargin shigo da makamai da suka kai N4bn

High court

An tsare wasu mutane 10 da hukuma hukumar leken asiri ta rundunar ‘yan sandan Najeriya suka kama, bisa zarginsu da hannu wajen safarar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma shigo da alburusai na Naira biliyan 4 bisa umarnin babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ranar Litinin.

An yi shigo da makaman ne a watan Yunin 2024.

Wadanda ake tuhuma goma da aka gurfanar a gaban mai shari’a Emeka Nwite sun hada da: Ali Ofoma, Okechukwu Charles, Kingsley Chinasa, Oroghodo Maxwell, Akinkuade Segun, Augustine Elechi, Osumini Kennedy, Ajala Ojo, Faboro Oluwatimilehin da Tolulope Ogundepo.

An gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a kan tuhume-tuhume shida da suka shafi ta’addanci, da shigo da makamai da sauransu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here