Kotu Ta Dage Sauraron Karar Atiku Abubakar Kan Zaben Shugaban Kasa

caaec1bd2bca942c
caaec1bd2bca942c

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, mai zamanta a birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis ta ɗage ɗage cigaba da sauraron ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar, suka shigar suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Kotun mai alƙalai biyar wacce mai shari’a Haruna Tsammani, ke jagoranta, ta ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 18 ga watan Mayu, domin cigaba da zaman fara sauraron ƙarar.

Lauyan masu shigar da ƙara, Cif Chris Uche, (SAN) ya gayawa kotun cewa sun zauna da sauran lauyoyin jam’iyyun, inda suka amince kan hanyoyin da za a bi domin tabbatar an kammala fara zaman sauraron ƙarar cikin nasara.

“Mai girma mai shari’a, lauyoyin jam’iyyun mun zaune tare, inda muka haɗa hannu wajen duba muhimman batutuwan da suka shafi fara zaman sauraron ƙarar.” A cewarsa.

A yayin da ya ke ɗage zaman sauraron ƙarar, mai shari’a Tsammani, ya yabawa ɓangarorin bisa haɗin kansu da matsayar da suka cimma, inda ya ce hakan zai taimaka wajen kammala zaman fara sauraron ƙarar, ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Atiku Abubakar, a cikin ƙarar da ya shigar tare da jam’iyyar PDP, mai lamba CA/PEPC/05/2023, yana neman a kwace satifiket ɗin cin zaɓen da hukumar INEC ta ba Bola Tinubu, na jam’iyyar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here