Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillers ta dakatar da mai horarwar ta Usman Shareef Abdallah na tsawon makonni 3.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa hakan na zuwa ne bayan da mai horarwar ya nuna halin ko in kula ga magoya bayan kungiyar sakamakon canjaras da kungiyar ta yi a hannun Bayelsa United a makon da ya gabata, kowacce kungiya na nema.
Hakan ne yasa kungiyar ta dauki matakin dakatarwar ga mai horarwar sakamakon nunawa magoya bayan halin ko in kula a wasan da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata.
Karanta labari mai alaka: EPL- Arsenal ta ragargaza Manchester City da ci 5-1
Kungiyar ta “Sai Masu Gida” dai ta samu nasara a wasa daya ne kawai cikin wasanni uku data buga a baya bayan nan.
Yanzu haka dai Ahmed Garba Yaro-Yaro, ne zai ci gaba da rike kungiyar a matsayin mai horarwarta a lokacin da Abdallah ke kan dakatarwarsa.
Sai kuma Abubakar Musa da Gambo Muhammad da Suleiman Shuaibu da kuna Ayuba Musa da za su kasance a matsayin masu taimaka masa.













































