Jami’an hukumar yaki da sha da fataucinyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama wani mutum Mai suna Qasim Ademola, wanda ke sarrafa wani abu mai gusar da hankali, wanda aka fi sani da Akuskura.
Jami’an yaki da miyagun kwayoyi ne suka kama shi da kwalabe dubu 26 da 600 na haramtattun kayan da aka tanada domin rabawa a fadin jihohin Arewa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
“An kama kayan ne a ranar Alhamis 15 ga watan Satumbar 2022 a gadar Tamburawa dake kan hanyar Zaria zuwa Kano, yayin da aka kama wani mai shekaru 39 daga karamar hukumar Akinyele, ta jihar Oyo tare da wasu mutum uku da ake zargin suke rarraba haramtattun kayan a wani samame da aka yi.” in ji sanarwar.
A halin da ake ciki, sanarwar ta ce jami’an hukumar sun kama wani tsohon mai laifin, Onyeka Charles Madukolu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja a Jihar Legas bisa laifin shigo da hodar ibilis wadda nauyinta ya Kai kilogiram 5 da digo 90 da aka boye a cikin gwangwani na deodorants.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Onyeka wanda aka yankewa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari a Kasar Habasha bisa laifin safarar miyagun kwayoyi kuma aka sake shi daga kurkuku a shekarar 2020, an sake kama shi a ranar Juma’a 16 ga watan Satumbar nan da muke ciki na 2022 a filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Legas lokacin da ya dawo daga Sao Paulo ya biyo ta Brazil ta Addis Ababa a wani Jirgin Kasar Habasha.
Sanarwar ta ce: ‘’A binciken da aka yi a kayansa an gano cewa ya boye hodar ibilis mai nauyin kilogiram 5 da digo 90 a cikin gwangwani na deodorants.
A yayin hira ta farko, ya yi ikirarin cewa ya shiga sana’ar sayar da miyagun kwayoyin ne don tara sabon jari da zai fara kasuwancin halal bayan an sake shi daga kurkukun Habasha a shekarar 2020.













































