Mutane 19 sun mutu a wani hadarin mota da ya auku a hanyar Abuja

20220918 165545 750x430 1
20220918 165545 750x430 1

Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 19 yayin da wasu takwas suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku ranar Lahadi a kan hanyar Yangoji zuwa Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja.

Mista Dauda Biu, mukaddashin Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta Kasa, shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a lokacin da ya ziyarci wurin da hatsarin ya afku.

Biu, ya ce hatsarin wanda ya faru a ranar Lahadi ya hada da motoci uku – guda biyu kira bas Toyota Hiace masu lambobi MUB- 30 LG da Kuma DWR-985 XJ da wata motar daban.

Biu, ya ce mutane 31 ne hatsarin ya rutsa da su da suka hada da maza 11, mace daya da kuma wasu 19 wadanda suka kone ba a iya gane su ba.

A cewarsa, motar kirar Toyota Hiace mai lamba MUB- 30 LG, ta afka cikin motar kirar Citroen nan da nan wuta ta kama, inda duk wadanda ke cikin motar suka mutu.

Biu, ya gargadi masu amfani da hanyar da su guji gudun wuce sa a, da sauran munanan halayen tuki.

Ya kuma gargadi masu ababen hawa da su rika tsara tafiye-tafiyen da suke yi a ko da yaushe da rana, sannan su guji tafiye-tafiye da daddare saboda hadurran da Ake yawan samu da daddare.

Ya kuma kara jaddada cewa rundunar za ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a masu ababen hawa tare da inganta ayyukan ta na sintiri domin dakile masu aikata laifukan tukii.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su rika kiran jami’an hukumar akan lamba 122 kyauta da gidan rediyon Traffic Rediyon FM akan mita 107.1 wanda a ko da yaushe masu amfani da hanya zasu iya samu don bayar da rahoton gaggawa a kowane lokaci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa, Mukaddashin Shugaban hukumar ya samu rakiyar tawagar gudanarwa da sauran jami’an ceto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here