Hukumar kula da Zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta bayyana cewa ta kama kayayyakin fasahar sadarwa (ICT) da darajarsu ta kai Naira miliyan 80, da ake zargin an sace daga wata makaranta a cikin birnin Kano.
Daraktan hukumar, Faisal Mahmud, ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin hukumar, Abubakar Ibrahim, ya fitar a ranar Laraba a Kano.
Ya ce tawagar sintiri ta hukumar ce ta kama kayan da aka sace daga ɗakin ICT na makarantar sakandiren gwamnati ta Aisha Shehu, Kuka, da ke karamar hukumar Fagge.
Mahmud ya ce barayin, waɗanda suka kai kimanin mutane 10, sun shiga ɗakin ne ta rufin sama, suka sace na’urorin kwamfuta, solar da sauran kayan.
Ya ƙara da cewa barayin sun mamaye masu tsaro na makarantar, suka daure su kafin su fara sata da misalin ƙarfe 2:00 na dare a ranar Laraba.
Karin labari: Kotunan Tafi-da-gidanka ta KAROTA ta kama direbobi 84 da suka karya doka a Danja
Hukumar ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda nan take ta tura jami’anta zuwa makarantar, amma da barayin suka ga motocin sintiri, sai suka ajiye kayan da suka sace suka tsere.
Mahmud ya jinjinawa jami’an hukumar bisa gaggawar amsa kiran gaggawa, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da haɗa kai da hukumar domin kare rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma, sanarwar ta rawaito shugaban makarantar, Rufa’atu Mahmud, tana yabawa hukumar bisa wannan kwazo.
Ta bayyana cewa kayan ICT ɗin an samar da su ne ƙarƙashin aikin AGILE da Bankin Duniya ya tallafawa, domin inganta ilimin fasahar zamani musamman ga ‘yan mata a jihar.
NAN












































