Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Kano sun kama fitacciyar mai amfani da manhajar nan ta TikTok, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin cin zarafi da lalata Naira.
An kama Murja Kunya ne da laifin fesa takardar kudin Naira domin jin dadi a lokacin da take zaune a dakin otal da ke Tahir Guest Palace a Kano.
Kamen dai ya biyo bayan farautar ta da jami’an EFCC suka yi mata, bayan da ta tsallake belin da hukumar ta yi mata tsawon wata daya da ya wuce.
Labari mai alaƙa: Hukumar EFCC ta kama shahararren ƴar TikTok Murja Kunya bisa zargin cin zarafin Naira
Tun da farko an kama ta ne a watan Janairun 2025 da laifin karya dokar babban bankin Najeriya CBN, dokar da ta haramta cin zarafi da lalata Naira.
Hukumar ta bayar da belin ta na wucin gadi har sai an gurfanar da ita a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano, sai dai lokacin gabatar da ita a kotu ya yi, amma Kunya ta gudu, ta kauce wa tsarin shari’a.
Sai dai kuma bayan kwashe tsawon makonni ana gudanar da bincike da sa ido, jami’an EFCC sun yi nasarar sake cafke ta a ranar Lahadi, 16 ga Maris, 2025. Daga nan kuma aka mika ta zuwa ofishin hukumar shiyya ta Kano, inda a halin yanzu take tsare tana jiran a gurfanar da ita a gaban kuliya.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta sake jaddada kudirinta na aiwatar da dokokin da ke kare mutuncin kudin Najeriya sannan ta yi gargadi kan ayyukan cin zarafi da suka hada da fesa, tambari, ko kuma lalata kudin a lokutan bukukuwa.