Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarni tare da umartar masu kadarorin da ke garuruwan Kwankwasiyya, Amana, da Bandirawo da su mamaye kadarorin su nan da watanni uku ko kuma ya kwace su.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin
Umarnin ya biyo bayan rantsar da sabon kwamishinan raya gidaje a gidan gwamnatin Kano.
Ya kuma bukaci wadanda ba za su iya zama ba da su bayar da hayar kadarorinsu, yana mai jaddada kudirin gwamnati na ganin garuruwan sun ci gaba.
Karanta: Dambarwar Masarautar Kano: Gwamnati za ta yi nazari tare da bin doka kan umarnin kotu
“Muna son wadannan garuruwa su habaka, shi ya sa muka samar da dukkan ababen more rayuwa da suka hada da tituna, ruwa, da wutar lantarki ta sa’o’i 24.
Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa Ma’aikatar Raya Gidaje ta Jiha za ta mamaye hedikwatar Hukumar Gidaje a halin yanzu yayin da Hukumar za ta koma birnin Kwankwasiyya domin kusantar gwamnati da jama’ar da take yi wa hidima.