Hukumar EFCC ta kama shahararren ƴar TikTok Murja Kunya bisa zargin cin zarafin Naira

WhatsApp Image 2025 03 16 at 16.31.46 750x430

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC reshen jihar Kano ta kama fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin yin amfani da kudin Naira wajen yin liƙi.

SolaceBase ta rawaito cewa wata majiya a hukumar EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja ne a ranar Asabar a Kano, inda ta kara da cewa ana gudanar da bincike.

“Ana ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da ita a gaban kotu” in ji majiyar.

Karanta: Zargin badaƙalar Naira biliyan 700: EFCC ta kama tsohon gwamnan Akwa Ibom Emmanuel

Majiya mai tushe ta shaida wa SolaceBase cewa an kama ta ne kimanin makonni uku da suka gabata amma ta yi yunkurin samun beli kafin a kama ta a jiya.

Murja Kunya ta fara shiga kafafen sada zumunta a matsayin abin sha’awa kafin ta mayar da ita sana’a.

Bayan lokaci, ta sami karɓuwa sosai, musamman akan TikTok, inda take aiki a ƙarƙashin sunan asusun Yagayagamen.

Ayyukanta na dandalin sada zumunta sun sha haifar da cece-kuce, lamarin da ya kai ga ana tuhumar t da yawa a jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here