Hukumar dake kula da gidajen gyaran hali ta kasa, ta dakile yunkurin shigar da miyagun ƙwayoyi gidajen yari

hali

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta yi nasarar dakile yunkurin shigar da miyagun kwayoyi zuwa gidajen yari.

Mai Magana da yawun hukumar reshen birnin tarayya Abuja, DSC Adamu Duza ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fita ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce “Bayan sanya ido da tsaurara bincike, mun damke dillalan muyagun kwayoyi a gidan gyaran hali da ke Kuje. Jami’an dake kula da tsaron Kuje Da misalin karfe uku na ranar Laraba, sun kama wani mutum mai suna Fidelis Emmanuel da wani abu da ake zargin tabar wiwi ce”

“A yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa wanda ake zargin ya zo da abinci a cikin kwano domin ziyaratar abokinsa da ke tsare. Ana cikin duba shi ne aka gano muggan kwayoyin da ya boye a kasan kwanon abinincin,kuma yanzu haka wanda ake zargin yana tsare”

Duza ya ce, Kwanturolan hukumar a Auja, Mista John Francis ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) domin daukar matakin doka a kanshi.

Ya ce, kwanturolan ya kuma kara tsaurara matakan tsaro da zasu sanya ido a cibiyoyin da ke cikin birnin tarayya Abuja, domin gano wadanda suke fakewa da ziyara suna safarar miyagun kwayoyi zuwa cibiyoyin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here