Hedikwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta yi magana kan jita-jitar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin amfani da ƙarfin soja a Jamhuriyar Nijar.
Hukumar tsaron ta Najeriya ta bayyana cewa ba ta samu wani umarni ba daga hukumomin da suka dace, domin yin amfani da ƙarfin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.
Hakazalika, hukumar tsaron ta bayyana cewa ba za ta iya yin aikin soji a ɗaya daga cikin ƙasashen ECOWAS ba har sai shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun sahale mata yin hakan.
Birgediya Janar Tukur Gusau, muƙaddashin darektan watsa labarai na hukumar, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a birnin tarayya Abuja, ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.
Gusau ya bayyana cewa rahoton ƙarya ce tsagwaronta, inda ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da shi, rahoton Vanguard ya tabbatar. Wani ɓangare na sanarwar na cewa: “Amfani da ƙarfin soja shi ne zaɓin ƙarshe idan har sauran hanyoyin da za a bi sun ƙare domin dawo da gwamnatin Jamhuriyar Nijar kan turbar amfani da kundin tsarin mulki.”
Ya kuma ƙara da cewa hafsoshin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun tattauna a birnin tarayya Abuja, domin miƙa shirye-shiryen da su ke da su ga shugabannin ECOWAS.













































