Hajj 2023: Saudiyya Za Ta Sauya Wa Alhazan Najeriya Hemomi

Mecca New
Mecca New

Hukumomin Saudiyya za su  sauya wa alhazan Najeriya 10,000 mazauni  a Muna sakamakon ƙarancin hemomin da suke fuskanta.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ce ta sanar da haka a ranar Talata.

Sanarwar da kakakin NAHCON Mousa Ubandawaki ya fitar, ta ce matakin ya biyo bayan ƙarancin hemomi da abinci  da alhazan Najeriya su kai kuka da su.

A ranar Litinin dai sai a ƙarƙashin gada wasu alhazan Najeriya suka riƙa fake wa zafin rana.

Mousa Ubandawaki ya ce jami’in Saudiyya mai kula da jin daɗin alhazan Najeriya ya nemi gafararsu kan halin matsin da suka shiga sanann ya ɗauki matakin kwashe 10,000 daga cikinsu zuwa hemomin alhazan Turkiyya waɗanda babu kowa a ciki.

A kowacce shekara dai Alhazai kan sauka a sansanin Muna kafin tsayuwar Arafa kuma nan suke dawo wa baayn Jifan Shaiɗan.

(Aminiya )

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here