Gwamnatin Tinubu Ta Sake Gayyatar Kungiyoyin Kwadago 

NLC
NLC

Gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta sake yin wani yunkuri na dakatar da yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke shirin yi a fadin ƙasar nan, yayin da gwamnati ta gayyaci shugabannin kungiyar domin sake tattaunawa.

Za a gudanar da taron ne yau Lahadi, 1 ga watan Oktoba.

A wata takarda da wani darakta a ma’aikatar ƙwadago, Emmanuel Igbinosun, ya fitar a madadin ministan, ya mika wa shugaban kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), an gayyaci shugabannin kungiyar taro a fadar shugaban ƙasa a ranar Lahadi.

A ranar Juma’a 29 ga watan Satumba ne gwamnatin tarayya ta shirya wani taro da kungiyoyin kwadago, amma shugabannin kungiyar ba su halarta ba, kuma taron bai yiwu ba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here