Gwamnatin tarayya ta yi gargaɗin mummunan Ambaliyar ruwa a jihohin Zamfara, Kano, Oyo da wasu 12

Floods sss

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin samun ruwan sama mai yawa tare da yiwuwar ambaliya a jihohi 15 da kuma al’ummomi 69 tsakanin ranar 24 zuwa 28 ga Satumba.

A cikin sanarwar da ta fito daga cibiyar fadakarwa da wuri kan Ambaliya ta ƙasa, wadda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta bayyana cewa wannan hasashe ya shafi jihohin Adamawa, Anambra, Bayelsa, Borno, Delta, Edo, Imo, Kano, Katsina, Ondo, Oyo, Ribas, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Al’ummomin da abin zai fi shafa sun haɗa da Yola, Yenagoa, Warri, Birnin Benin, Oguta, Kano, Jibia, Akure, Oyo, Ahoada, Shagari, Serti da Gusau da sauransu.

Gargadin ya ce idan aka samu ruwan sama mai yawa a waɗannan wurare, akwai yiwuwar ambaliya ta mamaye al’ummomin da wuraren da ke kewaye da su.

“Saboda haka, ana shawartar hukumomi da masu ruwa da tsaki su shirya yadda ya kamata tare da ɗaukar matakan kariya,” in ji Bokani.

An kuma bayyana cewa wannan gargadi wani ɓangare ne na tsarin sanarwa tun da wuri da ma’aikatar ke aiwatarwa don rage haɗarin rasa rayuka da dukiyoyi musamman a lokacin damina.

Labari mai alaƙa: NiMET ta yi hasashen samun ruwan sama da gajimare na tsawon kwana uku a Najeriya 

Haka kuma, mazauna wuraren da abin ya shafa, hukumomin ƙananan hukumomi da cibiyoyin bada agajin gaggawa an bukace su ɗauki matakan kariya.

Wannan gargadi ya biyo bayan ruwan sama mai yawa da ya mamaye wasu sassan birnin Legas kwanan nan, wanda ya janyo rugujewar gidaje, katse harkokin kasuwanci, tare da gurgunta manyan hanyoyi.

Ambaliya mai tsanani ta zama babban ƙalubale a Najeriya musamman a lokacin damina.

A shekarar 2022, ƙasar ta fuskanci mafi muni cikin shekaru goma, inda mutane sama da 600 suka rasa rayukansu, miliyan 1.4 suka rasa matsuguni, tare da lalata gonaki da dama.

Masana na danganta yawaitar faruwar ambaliya da sauyin yanayi, rashin ingantattun magudanar ruwa, da kuma gina birane ba tare da tsari ba.

Hukumomin (NiMet) da (NIHSA) tun da farko sun yi hasashen yiwuwar ambaliya a sassan daban-daban na ƙasar cikin shekarar 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here