Gwamnatin Kano ta rufe wasu rumfunan ajiye kaya guda biyu saboda gurɓata muhalli

WhatsApp Image 2025 05 03 at 11.04.01 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu rumfunan adana kaya guda biyu a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge bisa laifin keta ka’idojin tsaftar muhalli ta hanyar gurbata yanayi.

Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi Ismail Garba Gwammaja ya fitar a ranar Asabar ce ta bayyana hakan.

Sanarwar ta ce, rumbunan ajiyar da ke hanyar filin jirgin sama da ke kan titin Faransa, an gano cewa suna ajiye kayan kashe kwari da hayaki da ke fitar da muggan wari, lamarin da ke damun mazauna yankin da masu wucewa a kusa da wajen.

Daraktan hana gurbatar muhalli a ma’aikatar, Malam Ibrahim Nasir, wanda ya jagoranci gudanar da aikin, ya ce matakin ya biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka yi kan warin da ke fitowa daga ma’ajiyar.

Karin karatu: Shettima zai tafi kasar Gabon domin halartar bikin rantsar da shugaban kasa

“Bayan samun koke-koken, sai muka tura jami’an kula da muhalli domin gudanar da bincike, sakamakon binciken ya tabbatar da zargin, kuma an aika da sanarwar ragewa ma’aikatan wajen ajiyar kayayyakin, inda aka umurce su da su kwashe kayayyakin, rashin bin umarnin da suka yi ya sa aka rufe harabar, kuma an fara daukar matakin shari’a.” Inji Nasir.

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahiru M. Hashim, ya jaddada kudirin gwamnati na kiyaye lafiyar al’umma.

Dr. Hashim ya ce “Ajiye abubuwa masu haɗari a wuraren zama ko kuma al’umma yana haifar da haɗari ga muhalli da lafiya.

Ya kuma ja hankalin mazauna yankin da su kai rahoto ga hukumomin da suka dace, inda ya kara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da zage damtse wajen kare muhalli da bunkasar lafiya a jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here