Gwamna Yusuf ya taya takwaransa na Jihar Ekiti, Oyebanji, murnar rantsar da shi a wa’adi na biyu

IMG 20261017 WA0092 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya takwaransa na Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, murnar rantsar da shi a wa’adi na biyu a matsayin gwamnan jihar.

Gwamna Yusuf ya bayyana bikin rantsarwar a matsayin wani babban ci gaba a tarihin siyasar Oyebanji, tare da cewa hakan ya nuna irin amincewar da al’ummar Jihar Ekiti suka yi da shugabancinsa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Asabar.

Gwamna Yusuf ya bayyana fatan cewa wa’adin mulki na biyu na Oyebanji zai ba shi wata dama ta karfafa nasarorin da ya samu a baya, inganta tsarin dimokuraɗiyya da kuma hanzarta samar da ci gaban Jihar Ekiti.

Ya bukaci gwamnan na Ekiti da ya ci gaba da mayar da hankali kan manufofin da suka shafi bukatun al’umma, shugabanci da zai bai wa kowa dama da kuma shirye-shiryen da za su inganta rayuwar ’yan jihar.

Gwamna Yusuf, wanda mataimakinsa, Alhaji Murtala Sule Garo, ya wakilta a wajen bikin rantsarwar, ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi wajen karfafa hadin kan kasa, bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Gwamna Yusuf ya yi wa Gwamna Oyebanji da mataimakiyarsa, Monisade Afuye, fatan samun nasara da gudanar da wa’adi na biyu mai cike da ayyukan alheri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here