Gwamantin jihar Jigawa ta hana yanke bishiyun dake daji domin samar da gawayi ko ice, gwamantin ta yanke wanan wukuncin a wani matakin ta na kare ma’adane da abubuwan dake dajukan jihar.
Sanarwar hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Malam Lawan Ahmed, wanda da darakta ne a hukumar dake bawa mahalli kare a jihar (JISEPA), ya fitar yau Litinan a Dutsen jihar Jigawa.
Ya ce hukumar ta hana aikin yanke bishiyu da yake gudana batare da sahalewar hukumar ba.
“Hakkine akan JISEPA da ta dakatar tare da hana duk wani aikin yankewa ko sare bishiyu dake guduna a wanan jihar ba tare da sahalewar hukumar mu ba.”
“Mun samu rahotani daban daban cewa wasu matane na sare bishiyu da muke dasu a dajika domin samar da ice ko gawayi ba tare da amuncewr hukuma ba.”
Ya kara da cewa yawan sare bishiyun na jawo gurbatar yanayi, karancin ruwa da sarun abubuwa marasa dadi da ka iya jifa al’umma cikin wani hali mara kyau.
Ya kuma ja hankalin mazauna yankunan da abin yake faruwa da su bawa hukumar rahotan duk wanda suka ga yana irrin wanan aiki ba tare da iziniba.













































