Gidauniyar raya al’umma ta Lado (Lado Development Foundation – LDF) ƙarƙashin jagorancin Sanata Yakubu Lado Danmarke ta biya kuɗin rajistar ɗalibai talakawa sama da 17,888 na manyan makarantu a jihar Katsina.
Sakataren gidauniyar, Malam Muhammad Gali Salisu, ne ya bayyana hakan a jami’ar tarayya ta Dutsin-ma yayin tantance wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin.
Ya bayyana cewa gidauniyar tana aiki a fannoni da dama kamar ilimi, lafiya da kuma tallafawa al’umma don inganta rayuwar jama’ar jihar Katsina.
A cewar sa, a fannin ilimi, gidauniyar ta ɗauki nauyin ɗalibai tun daga makarantar sakandare har zuwa manyan makarantu domin ba su damar ci gaba da karatu.
Ya ce a bana gidauniyar ta kai ziyara jami’o’i da dama ciki har da jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato, jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kwalejin ilimi ta tarayya Zariya, kwalejin ilimi ta tarayya Katsina, jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta Katsina da sauran makarantun gaba da sakandare.
Sakataren ya bayyana cewa daga watan Janairu 2025 zuwa yanzu, ɗalibai 17,888 ne suka amfana da tallafin ilimi daga gidauniyar.
Ya ƙara da cewa a fannin lafiya, gidauniyar ta ziyarta asibitoci 50 tare da bayar da tallafin kuɗi ga marasa lafiya fiye da 5,873.
Ya ce gidauniyar ba ta nuna bambanci ba wajen biyan kuɗin rajista ga ɗalibai, domin tana biya ne ga kowa ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba.
Salisu ya bayyana cewa dangane da shirye-shiryen karatu, biyan kuɗin rajista yana tsakanin naira 25,000 ga ɗaliban NCE da ND, naira 42,000 ga ɗaliban digiri, yayin da ɗaliban digirin digirgir (PhD) ke samun tallafin har naira 235,000.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka amfana sun yaba da wannan taimako, inda ɗaya daga cikinsu, Sagir Sani, ɗalibi mai karatun ilimin zamantakewa, ya ce gidauniyar ta biya masa kuɗin rajista na naira 52,000, yayin da wata ɗaliba, Maryam Usman mai karatun MSc a fannin tattalin arziƙi, ta gode wa gidauniyar bisa biyan kuɗinta na rajista Naira 166,000.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan shiri na gidauniyar Lado ya kasance wani ɓangare na yunƙurin ci gaba da tallafa wa ilimi da walwalar al’umma a jihar Katsina.













































