Cikin Hotuna: ‘Yan baranda sun kone motoci, tareda toshe hanyoyi a kano

IMG 20230223 WA0002
IMG 20230223 WA0002

Wasu ‘yan baranda da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun kaddamar da kai hari kan magoya bayan ‘ya’yan jam’iyyar NNPP a kan hanyar Na’ibawa zuwa Zariya a Kano.

Rahotanni sun ce magoya bayan na kan hanyar zuwa Kwanar Dangora da ke wajen birnin domin tarbar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Alhamis lokacin da aka kai musu hari.

Kwankwaso na kan hanyarsa ta zuwa Kano ne domin gudanar da babban taron yakin neman zabensa na shugaban kasa a kano.

Akalla motoci 10 ya zuwa yanzu aka illata tareda kai hari yayin da aka kona wasu da dama.

Harin dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da jam’iyyun da ‘yan takararsu suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta biyu a Abuja.

Wani ganau da ya tsallake rijiya da baya, Tasiu Lawal, ya ce ya bi ta jikin wata babbar motar da yake ciki, ta hakane ya tsira.

“Na tsere da kyar Alhamdulillah. Sai aka ce mana su (’yan baranda) suna nan suna jiranmu, sai muka tsaya a Na’ibawa muka tabbatar muna da yawa kafin mu ci gaba da tafiya.

“Ba tare da sanin kowa ba, suka zo ta kowane bangare suka far mana. Sun fara kai mana sara da adduns ciki har da mata rike da adduna,” inji shi.

Jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, an tura su wurin da lamarin ya faru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here