Barazanar mamaya daga Trump: Mambobin ƙungiyar Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a Kano

IMG 20251108 WA0044 700x536 1 700x430

Mambobin ƙungiyar Musulmi a Najeriya (IMN), wadda aka fi sani da Shi’a, sun gudanar da zanga-zanga a manyan tituna na birnin Kano a ranar Asabar, suna nuna adawa da kalaman shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, wanda ya yi barazanar mamaye Najeriya don yaƙar ’yan ta’adda.

Masu zanga-zangar da suka rika tafiya a manyan tituna suna ɗauke da kwalaye da tutoci suna nuna rashin amincewa da ikirarin Trump cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.

Wasu daga cikinsu ma sun rika jan tutar Amurka a ƙasa, yayin da wasu ke ɗauke da hoton shugaban ƙasar Amurka da suka tanadar don nuna adawa da shi.

Trump a kwanakin baya ya ayyana Najeriya a matsayin “ƙasa mai matuƙar damuwa,” inda ya yi zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci ta hannun ’yan ta’adda, sannan ya gargadi cewa idan gwamnatin Najeriya ta gaza ɗaukar mataki, zai aika sojojin Amurka su dakatar da kisan.

Haka kuma ya ba da umarni ga ma’aikatar yaƙin Amurka da ta fara shirin yuwuwar kai hari a Najeriya.

Ƙungiyar Shi’a ta musanta kalaman Trump, tana kiran su karya ne da kuma tunzura jama’a.

A cikin wata sanarwa da Abdullahi Danladi na sashen albarkatun ƙungiyar ya fitar, ƙungiyar ta zargi ƙasashen yamma da yin amfani da yaɗa jita-jita domin haifar da rarrabuwar addini a Najeriya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa matsalolin ƙasar ba na addini ba ne, illa dai na cin hanci da rashawa da son kai na ’yan siyasa.

Ta kuma ce, Musulunci da Kiristanci duka suna koyar da ɗabi’a ta gari, amma wasu ke amfani da bambance-bambance domin cimma muradunsu na siyasa daga waje.

Mambobin ƙungiyar sun ce za su ci gaba da fafutukar wanzar da zaman lafiya da haɗin kan ’yan Najeriya duk da irin kalaman da suka kira masu tayar da hankali daga shugabannin kasashen yamma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here