Hukumar tabbatar da ingancin makarantun jihar Kaduna a ranar Juma’a, ta rufe wasu makarantun Islamiyyah guda biyu har illa masha Allahu bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara shida fyade tare da yi wa wata ciki ciki.
An rufe daya daga cikin Makarantun Madrasatul Ulumul Deeniya wa Tahfizul Qur’an da ke Rigasa bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara shida fyade a harabar makarantar.
Haka kuma ɗayar makarantar Islamiyya da ke Tsohon Masallacin Juma’a da ke Kachia, a karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, an rufe ta ne sakamakon zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 ciki da wani malami ɗan shekara 50 a makarantar yayi.
Shugaban Hukumar Mista Idris Aliyu, wanda ya rufe makarantar Islamiyyar da ke Rigasa, ya bayyana cewa an ci zarafin yarinyar ‘yar shekara shida a harabar makarantar kuma hukumar makarantar ta lulluɓe maganar tare da ikirarin ba ta da masaniya akan lamarin.
Aliyu ya ce bayanan da ke ma’aikatar ilimi sun nuna cewa kakar yarinyar ta je wurin hukumar makarantar ta kai kara amma dalibai da malaman makarantar sun lakada mata duka.
Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bayar da umarnin a rufe Islamiyya har sai an kammala bincike kuma a kama mai laifin.
“Shugaban makarantar zai dauki alhakin aikata wannan aika-aika har sai an bayyana sunayen duk mutanen da ke cikin makarantar sannan kuma yarinyar ta gano wanda ya aikata laifin kuma a hukunta shi,” in ji shi.
“Wadanda ke da alhakin cin zarafin kakar ta ma, musamman shugaban makarantar, suma za a gurfanar da su a gaban kuliya.”
“Wannan ya yi dai-dai da kudurin da gwamnatin jihar ke da shi na kare al’ummar da ba su da karfi a jihar,” inji shi.
Sai dai babban malamin makarantar, Malam Kabir Abdullahi ya musanta zargin, yana mai cewa “ba fyade ba ne.
“Abin da muka sani shi ne, wani yaro da ba a san ko wanene ba ya raunata yarinyar a al’aurarta da sanda,” in ji shi.
Abdullahi ya ce tuni DPO, Rigasa, ASP Abubakar Bauranya ya fara bincike kan lamarin.
DPOn ya tabbatar da karɓar karar kuma yayi daidai da labarin shugaban makarantar Islamiyya.
Sai dai kakar wadda aka aikatawa lamarin, Hajiya Batul Gambo ta dage cewa an ci zarafin jikanta, kuma an tabbatar da hakan ne daga Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Asibitin tunawa da Yusuf Dantsoho, Tudun Wada, Kaduna.
Wani rahoton likita da Dakta A Raji ya sanya wa hannu ya tabbatar da ikirarin Gambo na cewa an yi wa yarinyar ‘yar shekara shida fyade.
Da yake tsokaci kan fyade da ciki da aka yi wa yarinyar ‘yar shekara 12 a Kachia, Aliyu ya ce yarinyar na da cikin wata shida.
Ya ce an kuma rufe makarantar kamar yadda El-Rufai ya umarta, yana mai jaddada cewa ba za a iya tabbatar da tsaron lafiyar daliban ba.
Ya bayyana cewa kwamishiniyar aiyuka da jin dadin jama’a, Hajiya Hafsat Baba da kwamishiniyar ilimi Hajiya Halima Lawal za su hada kai da ‘yan sanda domin gudanar da bincike tare da tabbatar da an yi adalci.
“A halin da ake ciki, makarantun biyu za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike kuma a gurfanar da wanda ya aikata laifin bisa ga doka,” in ji shi.













































