Yan sandan jihar Katsina sun kama wani dan bindiga mai shekaru 30 da haihuwa, mai suna Sa’idu wanda aka fi sani da Sabon Jini.
Wanda ake zargin yana da hannu wajen kashe ACP Aminu Umar, Kwamandan ’Yan sandan Dutsinma na Jihar Katsina.
A ranar 5 ga watan Yuli ne ‘yan bindiga suka yi wa marigayi ACP Umar kwanton bauna suka kashe shi, a lokacin da yake jagorantar tawagar sintiri a aikin da aka saba yi na kawar da ‘yan ta’adda a yankin.
Rundunar ‘yan sandan da ke sintiri ta samu galaba a hannun ‘yan bindigar ne a wani kazamin artabu da suka yi da bindiga wanda a karshe ya yi sanadin mutuwarsa da na wani jami’in.












































