Amurka ta alkawarta ba da tallafin leƙen asiri da kayan tsaro ga Najeriya — Fadar Shugaban Kasa

Tinubu Trump

Gwamnatin ƙasar Amurka ta bayyana aniyar ƙarfafa haɗin-gwiwar tsaro da Najeriya, ciki har da samar da ƙarin tallafin leƙen asiri da kayan tsaro domin ƙarfafa ayyukan yaki da ‘yan ta’adda da kungiyoyin masu tayar da hankali a ƙasar.

Wannan ya biyo bayan tattaunawa da wasu muhimman ganawa da wata babbar tawagar gwamnatin Najeriya ta yi da jami’an ƙasar Amurka a makon da ya gabata domin faɗaɗa yarjejeniyar tsaro tsakanin ƙasashen biyu da kuma buɗe sabbin hanyoyin haɗin kai.

Tawagar, karkashin jagorancin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ta gana da manyan jami’ai a majalisar dokokin Amurka, ofishin bangaren addini na fadar shugaban kasa, ma’aikatar harkokin wajen Amurka, majalisar tsaro ta ƙasa da kuma ma’aikatar yaƙi ta ƙasar.

Mambobin tawagar sun haɗa da lauyan gwamnati Lateef Fagbemi; shugaban hafsoshin tsaro Janar Olufemi Oluyede; shugaban leƙen asirin tsaro Laftanar Janar Emmanuel Undiandeye; sufeto janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun; da wakilai biyu daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro.

A cewar sanarwar da mai ba shugaban kasa shawara kan bayani da dabarun sadarwa Bayo Onanuga ya fitar, tawagar ta yi bayanin cewa rikice-rikicen da ake samu a ƙasar na shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, tare da ƙaryata duk wani zargin kisan kare dangi.

Karanta: Garkuwa da ɗalibai a Makarantu na barazana ga samun Ilimi a Arewa – Amnesty ta yi gargadi

Sanarwar ta bayyana cewa tattaunawar ta taimaka wajen gyara kuskuren fahimtar abin da ke faruwa a Najeriya, ta ƙarfafa amincewar juna da kuma gina haɗin-gwiwa mai dogaro da mafita, musamman wajen kare al’ummomin da ke fama da hare-hare a yankin tsakiyar Najeriya.

Haka kuma, gwamnatin Amurka ta nuna shirinta na ƙarin tallafi, ciki har da agajin jinƙai ga al’ummomin da abin ya shafa da kuma taimakon fasaha domin ƙarfafa tsarin gano matsalolin tsaro da wuri.

A gefe guda, tawagar Najeriya ta sake tabbatar da kudirin gwamnati na ƙara inganta kariyar fararen hula.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnati na sane da yadda batutuwan tsaro da ‘yancin addini ke da mahimmanci ga jama’a, tare da tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa ana ɗaukar matakai na gaggawa da tsari domin tabbatar da tsaron ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here