ACF ta Buƙaci ’yan Najeriya su riƙa neman bayanin ayyukan shugabanninsu

Images 2

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci ’yan Najeriya da su riƙa ɗora wa shugabannin siyasa alhakin ayyukansu, musamman wajen magance matsalolin tsaro, talauci, matsin tattalin arziki da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar.

Shugaban ƙungiyar, Mamman Osuman, ne ya yi wannan kira a saƙonsa na taya ’yan Najeriya murnar bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun ƙarin mutanen da suka rasa matsugunansu, durƙushewar harkokin tattalin arziki, rufe makarantu da lalacewar hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin mawuyacin halin da ’yan Najeriya ke ciki, an haddasa su ne ko kuma ƙara ta’azzara su ta hannun mutanen da aka damƙa wa alhakin shugabanci da gudanar da mulki.

“Abin takaici, wasu daga cikin waɗannan mawuyacin yanayi na rashin tausayi, mutanen da muka damƙa wa alhakin shugabanci da gudanar da mulki ne ke haddasawa ko kuma ƙara ta’azzara su. Wannan yanayi na buƙatar zurfafa tunani.

“Shugabanci amana ce mai girma. Waɗanda aka damƙa wa ikon gudanar da gwamnati dole ne su riƙa tuna cewa an ba su waɗannan muƙamai ne a matsayin amana daga al’umma, domin amfanin jama’a baki ɗaya,” in ji shi.

Osuman ya jaddada cewa ya kamata a ɗauki shugabanci a matsayin amana mai girma, ba wata hanya ta biyan buƙatun kai ko cimma muradun mutum ba.

Yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, ya buƙaci ’yan ƙasa da suka cancanci kaɗa ƙuri’a da su mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC), tare da shiga cikin harkokin zaɓe yadda ya kamata.

Sai dai ya gargaɗi masu zaɓe da kada su riƙa yanke shawarar wanda za su zaɓa bisa umarnin jam’iyyun siyasa kawai, inda ya buƙace su da su duba tarihin ayyukan ’yan takara, manufofinsu da kuma matsalolin da ƙasar ke fuskanta kafin su yanke shawarar wanda za su mara wa baya.

“Ya kamata ƙuri’unmu su kasance bisa nazarinmu na kanmu, lamirinmu, hukuncinmu da kuma tantance ’yan takara da batutuwan da suka shafi ƙasa, maimakon kawai bin kiraye-kirayen ko umarnin kowace jam’iyyar siyasa.

“Ƙuri’ar kowane ɗan ƙasa wata hanya ce ta bayyana zaɓinsa na kansa, sannan kuma wata dama ce da kundin tsarin mulki ya ba shi domin tantance wanda ya kamata a damƙa wa alhakin jama’a. Saboda haka, mu riƙa kaɗa ƙuri’a cikin sanin ya kamata, lumana da kyakkyawan tunani,” in ji Osuman.

Shugaban ACF ɗin ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar barkewar tashin hankali da ya shafi zaɓe, inda ya yi kira ga ’yan siyasa da sauran ’yan ƙasa, musamman matasa, da su riƙa taka-tsantsan kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan kammala zaɓe.

Haka kuma, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da kalaman siyasa masu tayar da hankali, tsokana da kuma lalata rayuka da dukiyoyi.

Ya bayyana cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya haifar da ƙiyayya ko tashin hankali ba.

“Saboda haka, ina kira ga dukkan ’yan ƙasa, musamman matasanmu, da su kasance masu natsuwa, tare da guje wa wurare, taruka da abubuwan da aka sani ko ake da zargin akan su cewa za su iya haifar da tashin hankali.

“Babu wani zaɓen siyasa da ya cancanci a rasa ran mutum saboda shi. Mu yi watsi da tashin hankali, kalaman tunzura jama’a, tsokana da lalata rayuka da dukiyoyi. Bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama sanadin ƙiyayya, tashin hankali ko lalata garuruwa ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa tabbatar da makomar ƙasar mai kyau na buƙatar haɗin kai da ɗaukar nauyi daga gwamnati da kuma ’yan ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here