An rufe rumfunan ajiya guda biyu da ake zargin alkama ba ta da inganci a kasuwar Kano
Kungiyar yan kasuwar Dawanau dake jihar Kano ta sha alwashin kule hukunta duk wanda suka kama da shigu da kayan abinci marasa inganci cikin kasuwar.
Solacebase ta rahoto cewa kungiyar yan kasuwar sun sha alwashin ne sakamakon kama sama da kwantena 50 na kayan abinci mara kyau a kasuwar.
Yayin wani samame da jami’an kasuwar suka yi tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ayyukan Noma, an rufe rumfunan ajiya guda biyu dauke da buhunan alkama kimanin 2,000 da ake zargin ba su da inganci.
Jami’an kasuwar sun bayyana cewa kungiyar ta kafa wani kwamiti da zai gano tare da kamo masu laifin domin a sanya musu takunkumi da kuma gurfanar da su gaban kuliya.