Zaɓe: A kasa, a tsare, a raka ba zai yi aiki ba wannan karon – INEC

FB IMG 16770668497289481
FB IMG 16770668497289481

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce tsarin a kasa a tsare, a raka ba zai yi aiki ba a zaɓen bana.

INEC ta shaida hakan ne a wata tattaunawa da BBC ta yi da jami’an ta, a ci gaba da kawo bayanai kan muhimmancin abubuwa da ya kamata a sani ko tunatarwa kafin ranar zaɓe.

Hukumar INEC ta ce a yanzu sai dai a ce a kasa a tsare a rumfar zaɓe, saboda komai zai kasance cikin na’ura wanda za a riƙa aikewa kai-tsaye zuwa cibiyar tattara sakamako.

Hajiya Zainab Aminu Abubakar da ke magana da yawun hukumar ta ce ta yanar gizo za a rinƙa aike sakamakon zaɓen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here