An aike da mutumin da aka kama da katinan zaɓe 29 zuwa gidan yari a Kano

327370013 893830768489657 8743347781602791459 n
327370013 893830768489657 8743347781602791459 n
Wata kotun majistare a Kano ta tasa keyar Tasiu Abdullahi zuwa gidan yari har sai an yanke hukunci kan neman belinsa.
A kwanakin baya ne ‘yan sanda su ka kama Abdullahi, mai shekaru 45, da katinan zabe na dindindin guda 29, mallakar wasu al’umma a karamar hukumar Dawakintofa ta jihar Kano.
Daily Nigerian ta rawaitu cewa lauya mai shigar da kara, Hadiya Ahmad, ta ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin da ya sabawa sashe na 22 na dokar zabe ta 2022.
Sai dai Abdullahi ya musanta aikata laifin.
Don haka lauyansa MB Baba ya mika bukatar neman belinsa, amma mai gabatar da kara ya ki amincewa da bukatar.
Daga nan ne Alkalin Kotun Mai shari’a Mustapha Saad-Datti ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan neman belin wanda ake zargin, sannan ya bayar da umarnin a tsare wanda ake tuhuma ɗin a gidan yari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here