Allah ya yi wa mataimakin shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max Airline Alhaji Bashir Barau Mangal rasuwa.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar SOLACEBASE cewa Bashir Mnagal ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a, a Abuja bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
“Za a yi Jana’izar Marigayin Kamar yadda Addinin muslunci ya tanada a birnin Katsina da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar juma’a 23 ga watan Disambar shekarar 2022,” a cewar majiyar.












































