Kwanaki shida kenan da fara yawon sababbin kudade a fadin kasar nan, wasu daga cikin ‘yan kasuwa sunki karbar su.
Sababbin kudin da aka sake N1,000, N500 da kuma N200 sun fara yawo a 15 ga watan Disamba na wanan shekarar.
26 ga watan watan Oktoba, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sanar da aniyar bankin na sake sauyawa fasalin kudin Najeriya launi, sanan kuma kuma ya ce za’a daina karbar tsofafin kudi a karshen watan Jinairu na sabowar shekara.
Wani mai saida abinci, Sofiat Balogun ya ce zai jira lokaci kadan kafin ya fara karbar sabbabin kudadin.
“Naji jama’a na cewa kudadin bama masu kyau bane, sanan kuma kudin basu zaga ku ina na a fadin Najeriya ba.”
“Na ga vedio da dama na jabun kudin na yawo a shafikan sada zumunta, hakan yasa gaskiya inajin tsorun karbar su.”
Eme Jackson, shima wani bawan Allah ne mai saida kayan marmari, ya ce gaskiya ba zai taba karbar sababbin kudin ba, saboda sunyi haske da yawa.
“Na zabe danayi amfani da tsofafin kudi saboda sunfi karfi da nagarta akan sabbabin”













































