Marwa: Gwani abin koyi ya cika Shekara 69 – Femi Babafemi

marwa NDLEA
marwa NDLEA

Fassarawa:Aminu Bala Madobi-Daga Kano

Fiye da shekaru ashirin kenan, Muhammad Buba Marwa ya kasance wani jigon tauraro abun tattaunawa ako da yaushe la’akari da sadaukarwa da jarumtaka da ya nuna a salon jagoranci na kwarai abin kwatance

Wadanda suka gabata sun ce jagorancin da marwa yayi na daya daga cikin manyan misalan jagoranci nagari da ya nuna a lokacin yana cikin kaki da sojoji ke mulkin kasar nan.

A da har ma da yanzun, anta yin munana da kalaman kiyayya ga salon da Marwa ya dauka a matsayin wani misali na ingantaccen jagoranci ga jamaa.

Sai dai kamar yadda abubuwa akoda yaushe ke canzawa, Marwa ya sake samun dama la’akari da Kwarewar sa da ta bayyana afili a ranar 15 ga Janairu 2021, lokaci kenan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Birgediyan Mai ritaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa.

Watanni ashirin bayan nadin Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya tabbatar da kwarewar da yake da ita nayin aiki kan-jiki-kan-karfi dan sauke nauyin aikin a aka dora masa. Marwa azuwan sa hukumar ya shigo da sabbin jini abokan aiki tare da nuna jajircewar sa na shugabancin hukumar ta NDLEA.

A yau, Buba marwa ya kasance abin labari a zamanin baya na “Sihirin Marwa a Legas,” wanda yanzu shine labarin zamaninmu kamar yadda Marwa ya sauya fasalin hukumar NDLEA ta ke ta aiki ba kama Hannun yaro.

Hakika Marwa ya rike manyan ofisoshi da dama a zamaninsa, wadanda suka hada da Gwamnan Soja na Tsohuwar Borno tsakanin 1990-1992, Magatakardar Makarantar Sojoji ta Najeriya tsakanin 1992-1993 dakuma Shugaban dakarun soji na Legas tsakanin 1996-1999.

Tabbas babu mamaki, bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban Nijeriya da kuma baiwa bil’adama dama, a yau Janar Marwa yana da mukaman sarakunan gargajiya 19 a fadin kasar nan.

Marwa ba ya shakkar ko yin gezau wajan tunkarar kowanne irin kalubale, ta yadda ya kara fadada hukumar ta hanyar samar da sabbin daraktoci shida, dakuma shugabannin shiyoyi 14, da kuma runduna ta dabarun yajin aiki da dai sauransu.

A baya a cikin shekarar akif 1997, mujallar Newswatch ta yaba masa a matsayin gwarzon Shekar kana bayan shekaru 24, ya kasance gwarzon jaridar “Man of the Year” na 2021.

A cikin shekarar da ta gabata ne, ya sami lambobin yabo tareda karramawa da ya samu a kafafen labarai akalla 10 bisa ga nagartar salon jagorancin shi ga Hukumar.

Wannan mutumin da ake batu, Buba Marwa ke cika shekaru 69 a yau. A irin wannan rana, da mutum zai yi fatan ya zauna tare da iyalai dangi da masu yimasa fatan alheri don yin bikin, amma kash! yana can kasar Amurka dan cigaba da ƙarfafa danganta da takwarori abokan hulɗarmu, dan cigaba da inganta aikin hukumar tayi shura a idanun duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here