Za’a kammala kashin farko na aikin titin Kano zuwa Katsina a shekarar 2022- Minista

Kano Katsina rd
Kano Katsina rd

Gwamanatin tarayya ta ce zata kammala kashin farko na aikin titin Kano zuwa Katsina kafin karshen wannan shekarar.

Ministan aiki da gidaje, Umar El-Yakub, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai Kano ranar Asabar.

Ya ce an fitar da aikin tun a shekarar 2013, ya kara da cewa kammala aikin na daya daga cikin nasarorin da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu.

El-Yakub ya kuma yi kira ga ‘yan Kwangilar da su yi kokari su kammala gadar Yakasai -Badume, da zarar damuna ta wuce.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here