Kungiyar SERAP ta shigar da Gwamnonin Jihohin kasar nan 36 gaban Kotu

SERAP
SERAP

Kungiyar rajin tabbatar da daidaito a ayyukan gwamanti (SERAP) ta shigar da karar gwamnonin jihohin kasar nan 36 kan kudaden da aka ware domin biyan tsofaffin gwamnonin kasar nan fansho.

Kungiyar ta SERAP ta bayyana kudaden fanshon da za a biya tsofaffin gwamnonin a matsayin abinda baai kamata ba, inda ta ce, kamata ya yi a yi amfani da kudaden domin baiwa yaran talakawa damar samun ingantaccen ilimi a jihohinsu.

A cikin kara mai lamba FHC/L/CS/1120/2022 da aka shigar a makon jiya a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman “umarni da tilasta wa gwamnonin jihohi 36 da su biya kudaden da ‘Ya ’yan talakawa su yi amfani da su don samun ingantaccen ilimi a jihohinsu.”

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa an biya sama da Naira biliyan 40 ga tsofaffin gwamnoni 47 daga jihohi 21 daga cikin 36 na fansho da samar da gidaje da ma’aikata da canza motoci.

SERAP ta ce, “Gwamnonin Jihohi na biyan tsofaffin gwamnonin jihohinsu biliyoyin Naira na fansho da sauran alawus-alawus, a yayin da suke gaza zuba jari a fannin ilimi da kuma biyan kudaden da za su baiwa yaran Najeriya marasa galihu da ke jihohinsu damar samun ingantaccen ilimi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here