Masarautar Katsina ta sanar da suke hawan babbar sallar bana, wanda ya kamata ayishi ranar Asabar.
Sanarwar suke hawan na bana, na dauke cikin wata sanarwa da mataimakin sakataran masarautar Alhaji Sule Mamman-Dee ya sawa hannu.
Mamman-Dee ya ce an suke hawan sallar ne saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da ita, inda ya kara da cewa Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir-Usman ya damu da matsalar tsaro sosai, zai hallar ce sallar Idi ne kadai.
Ya kuma bukaci Muslims dasu ci gaba da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya mai durewa












































