Labari da dumi dumi: Mataimakin shugaban kasa Yami Osinbajo bai yi hatsari ba

FB IMG 16545261184814539
FB IMG 16545261184814539

Mai magana da yawun Farfesa Yemi Osinbajo kan harkar yaɗa labarai Laolu Akande, ya karyata labarain da ake yaɗawa a kafafan sada zumun ta cewa mataimakin shugaban ƙasar ya yi hatsarin mota.

A yau dai Litinin mutane suka fara Yada labarin cewa wai Farfesa Osinbajo ya yi hatsari mota a kan hanyarsa ta zuwa jihar Ondo domin jajanta wa iyalan waɗanda aka kai wa hari a Cocin Francis a Owo a jiya Lahadi.

A wata sanarwa da yayi a kafar sada zumin ta tuwita, kakakin Mataimakin shugaban kasan ya ce Osinbajo ya hadu da wani hatsari ne da aka yi a hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukar jiragen sama dake garin Abuja, inda ya tsaya domin ya bada taimakon gaggwa ga waɗanda abin ya shafa.

Inda ya ƙara da cewa tuni har Osinbajo ya isa jihar Ondon domin gudanar da abinda ya kai shi jihar.

“Mataimakin shugaban ƙasar ya ga an yi hatsari ne a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama da safiyar yau, inda ya tsaya domin yabada agaji wajen tsara yadda za a kai mutanan zuwa asibiti a motar ɗaukar marasa lafiya ta jerin a yarin motocinsa.

“Daga nan sai ya wuce don tafiyar tasa zuwa Ondon.

A wani bangaran, Ita ma hukumar kula da kare afkuwar haɗurra ta kasa Najeriya ta ƙaryata batun cewa Osinbajo ya yi hatsari, kamar yadda aka yi ta yaɗawa a kafafen sada zumunta.

3 SHARHI

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here