Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Kano, ta yi tir da harin da aka kai wa ‘yan jarida da ke aikin dauko rahoton taron jam’iyyar APC a Filin Wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar Asabar.
Kungiyar ta bayyana lamarin, wanda ake zargin wasu ’yan daba ne suka kai wa ‘yan jarida hari tare da lalata motar gidan rediyon kasa, Pyramid FM a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, kuma barazana ce babba ga ’yancin aikin jarida.
NUJ ta jaddada cewa bai kamata a kai wa manema labarai hari, tsoratarwa ko hantara yayin da suke gudanar da halataccen aikin su ba.
A cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Comrade Suleiman Abdullahi Dederi, da Sakatarensa, Comrade Hauwa Suleiman Zahradeen, suka sanya wa hannu a ranar Asabar, kungiyar ta ce ta damuwa matuka saboda lamarin ya faru ne a lokacin wani taron siyasa, a daidai lokacin da lamuran siyasa ke kara karuwa gabanin zaben 2027.
“Kai hari ga ‘yan jaridu da ke ruwaito lamuran siyasa ba kai hari ga kafafen yada labarai ba ne kawai, koma baya ne ga dimokuradiyya. Domin ‘yantacciyar kafar yada labarai mai zaman kanta tana da matukar muhimmanci wajen fadakar da jama’a da kuma gudanar da dimokuradiyya mai gaskiya,” in ji sanarwar.
“‘Yan jaridu su ne muhimman masu ruwa da tsaki a kowace al’umma da dimokuradiyya.”
“Ayyukansu shi ne sanar da jama’a, samar da dandalin bayyana ra’ayoyi daban-daban da kuma ruwaito ayyukan siyasa ba tare da nuna son rai ba.”
“Saboda haka dole ne a ba su damar gudanar da wadannan ayyuka ba tare da tsoron tashin hankali, tsoratarwa ko tsangwama ba.”
“Kungiyar NUJ ta Jihar Kano ta damuwa matuka game da tsaron ‘yan jaridun da ke ruwaito ayyukan siyasa, musamman a lokacin manyan taruka inda ‘yan jaridu ke fuskantar hadari.”
“Gaskiya ne cewa maharan sun yi amfani da adda da wuka wajen lalata motar Radio Nigeria, duk da kasancewar jami’an tsaro a cikinta, abin da ya kara dagula lamarin ne., hakan tasa bukatar gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa.”
Kungiyar ta jajantawa shugabannin gudanarwa da ma’aikatan Radio Nigeria, Pyramid FM Kano kan harin da aka kai da kuma barnar da aka yi wa motarsu.
Haka kuma ta jajantawa dukkan ‘yan jaridu da sauran mutanen da ke cikin motar da aka jefa su cikin tsoro da tashin hankali.
Duk da cewa kungiyar ta yaba da kokarin jami’an tsaro wajen kiyaye zaman lafiya a tarukan jama’a, ta bukaci su gudanar da bincike mai zurfi na gaskiya kan harin, inda ta ce su gano da kuma kama wadanda suka aikata laifin, sannan duk wanda aka samu da laifi ya fuskanci hukunci bisa doka.
NUJ ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jaridu da tsarons, tare da ci gaba da tattaunawa da hukumomi da masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa ‘yan jaridu a Kano za su iya gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ba.












































