Sarkin Zurmi a Jihar Zamfara, Alhaji Bello Suleiman, ya rasu bayan shekara biyar a kan karagar mulki.
Mai Martaba Sarkin ya rasu a ranar Litinin da yamma a Asibitin Kwararru na Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, kamar yadda masarautar ta sanar a cikin wata takarda.
Suleiman ya hau sarauta a shekarar 2021 bayan rasuwar kawunsa, Abubakar Atiku, wanda Gwamnatin jihar ta cire a wannan shekarar sannan ta sauke shi bisa ka’ida a watan Afrilu 2022.
An cire Atiku tare da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar bayan an zargi sarakunan biyu da alaka da ‘yan bindiga da kuma tsoma baki cikin ayyukan tsaro, sannan daga baya Atiku ya rasu a wani asibiti a kasar Masar.
Marigayi Sarkin Zurmi, Suleiman, ya yi mulki ne a lokacin da rashin tsaro ya tsananta a Zurmi.
A watan Mayun 2024, ‘yan bindiga sun kai hari garin, inda suka shiga fadar sarkin tare da kashe jami’an tsaro 3 da ke tsaye a kofar fada sannan sun yi garkuwa da wasu mazauna.
Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai babban jami’in tsaron sarkin, Buhari Yusuf da wasu maza biyu, Aliyu Ahmed da Sa’idu Lawali.
‘Yan bindigar sun kuma lalata wata cibiyar sadarwa domin katse sadarwa da hana jami’an tsaro amsa kira cikin gaggawa.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun zargi marigayi sarkin da kasa yin wani abu kan zargin zaluntar ‘yan Fulani da ‘yan bangar gari ke yi.
Zurmi na kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar kuma yana da iyaka da Jihar Katsina gari na biyu mafi yawan jama’a a Jihar Zamfara bayan Gusau.












































