‘Ya’yan El-Rufai sun yi cacar baki, Bashir ya zargi Bello da shan giya da hodar iblis

Bashir and Bello 750x430

Bashir El-Rufai, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya zargi yayansa kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai, da sanya muradunsa na siyasa a gaba maimakon biyayya ga iyalai a dangantakarsa da Gwamna Uba Sani.

SolaceBase ta ruwaito, Bashir ya yi wannan zargin ne a wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar.

Lamarin ya faru ne yayin wata muhawara game da dangantakar siyasar Bello da Sani, da kuma shawararsa ta bin mahaifinsu zuwa jam’iyyar ADC.

A cewar Bashir, Bello ya ci gaba da kasancewa tare da Uba Sani a mafi yawancin lokutan da gwamnan da Nasir El-Rufai suke takaddama da juna, inda ya bayyana cewa Bello ya dawo kusa da sansanin siyasar gidan ne kawai bayan da aka zargi cewa dangantakarsa da Sani ta lalace.

“Ya makale a wurin Uba Sani har sai da ya gane cewa za a kore shi, sannan ba zato ba tsammani ya tuno da biyayya ga iyali ya kuma koma ADC, da yana ina? Muradun kansa ne kawai a gabansa,” in ji Bashir.

Haka kuma, ya zargi dan uwan nasa da neman ya daina sukar Sani, wanda Bello ya taba yi wa aiki a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin majalisa lokacin da gwamnan yake sanata.

Bashir bai nuna alamun amincewa da wannan bukatar ba, inda ya bayyana a wani saƙon cewa: “A wannan matakin na rayuwata, na tsani shirme.”

A wani sakon na daban, Bashir ya yi zargin cewa Bello ya gaya masa cewa ya je ya kashe kansa.
“Gaya mini yake in kashe kaina,” in ji shi.

Wannan cacar baki ta janyo martani daga sauran masu amfani da shafin X.

Wani mai amfani da kafar mai suna Nurudeen Adamz (@baldeenadamz), ya kalubalanci shawarar Bello na tattauna batutuwan iyali a kafofin sada zumunta, inda ya rubuta: “Da ni ne shi, da da kaina zan kashe ka.”

Bashir ya kuma bayyana cewa yana ajiye bindigogi da wukake a gefen gadonsa, kodayake ba a tantance ainihin mahallin da ya sa ya fadi hakan ba.

To sai dai kuma, al’amarin ya wuce batun dangantakar siyasa tsakanin Bello da Sani kawai.

A wasu sakonnin da aka goge, an ruwaito cewa Bashir ya yi wasu jerin wasu zarge-zarge na kashin kai masu tsanani a kan dan uwan nasa, ciki har da zargin cewa Bello yana shaye-shayen giya da hodar iblis.

Haka zalika, sakonnin da aka goge din an ce sun kunshi zargin da ke alakanta Bello da mutuwar daya daga cikin ‘yan uwansu, tare da sauran kalamai na sirri game da iyalinsa da rayuwarsa ta sirri.

Ba a sami damar tantance sahihancin zarge-zargen da ke cikin sakonnin da aka goge ba, yayin da sakonnin ba sa nan a shafin X na Bashir a lokacin da ake hada wannan rahoto.

An kuma ruwaito cewa Bashir ya yi wa dan uwan nasa kashedi mai ban tsoro a daya daga cikin sakonnin da ya goge, inda ya shaida masa da ya fita daga harkoshinsa, yana mai nuni da cewa duk wata arangama tsakaninsu na iya yin sanadiyyar mutuwar dayansu.

Wannan takaddama ta canza abin da ya fara a matsayin sabanin siyasa zuwa babban rikici na kashin kai tsakanin ‘yan uwan guda biyu.

Sauran sakonnin Bashir da ba a goge ba, sun nuna cewa rashin jituwar na da alaka da babban rikicin siyasa da ke tsakanin mahaifinsu da Gwamna Sani.

Bello ya yi aiki a matsayin mataimakin Uba Sani tsakanin 2019 zuwa 2023 lokacin da Sani yake sanata, daga baya ya lashe zaben majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa.

Uba Sani ya gaji Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan Kaduna a shekarar 2023, amma dangantaka tsakanin ‘yan siyasar biyu ta lalace bayan mika mulki.

Daga baya Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC ya kuma koma ADC, yayin da Bello ya bi sahun mahaifinsa zuwa jam’iyyar adawa ta ADC.

Sai dai Bashir ya kalubalanci amincin siyasar dan uwan nasa, inda ya kafa hujjar cewa Bello ya koma ADC ne kawai bayan dangantakarsa da Sani ta yi tsami.

Ya kuma bayyana cewa yayin da wasu daga cikin iyalinsu ke fuskantar gwamnatin Sani a bayyane, Bello ba ya cikin wannan kokarin.

Wannan dambarwa na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ke fuskantar kalubalen shari’a da na siyasa.

Tsohon gwamnan na fuskantar tuhuma a gaban kotuna a Abuja da Kaduna kan zarge-zargen da Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki Tu’annati da Wasu Laifuka Masu Alaka (ICPC) ta shigar, da suka hada da zargin cin hanci da rashawa da kuma cin zarafin matakin iko.
Haka kuma yana fuskantar wata shari’ar daban a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja game da zargin sakon waya na sirri, a cikin wata shari’a da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta shigar.

Bashir, a wani sako na daban, ya ce ko da mahaifinsa ya yafe wa wadanda yake amanna sun kai wa iyalinsu hari, shi kansa ba zai yafe ba.

“Ko da mahaifina zai fito daga wannan jarrabawar kamar Gandhi kuma ya yafe ya kuma manta, ni ba zan yafe ba,” in ji Bashir.

Ya kara da cewa kamata ya yi wadanda yake gani da laifin kai wa iyalinsu hari su fuskanci sakamako, ban da dan uwansa, Mahmud Ribadu, wanda ya bayyana a matsayin dan uwansa na jini.

Wadannan kalamai na baya-bayan nan sun kara fito da zurfin baraka da ke tsakanin iyalin El-Rufai yayin da ake ci gaba da sauya sheka da rarrabuwar kawuna a siyasa gabanin babban zaben 2027.

Bello El-Rufai bai mayar da martani a bainar jama’a ba game da wadannan zarge-zarge a lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here