Fadar Shugaban Kasa a ranar Asabar ta fitar da jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC gabanin zaben shekarar 2027.
An tsara gudanar da zaben shugaban kasar a watan Janairu 2027, bisa ga jadawalin da Hukumar Zabe ta INEC ta fitar.
A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan Yada Labarai da Dabaru ya sanya hannu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai kasance Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben, yayin da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, wanda ake sa ran zai kasance abokin takararsa a zaben 2027, zai kasance Mataimakin Shugaban kwamitin.
An nada Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, mataimakin shugana kwamiti na biyu.
An kuma nada tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na yakin neman zaben, tare da Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar, Hope Uzodinma, a matsayin Sakataren Kwamitin.
Sakatariyar Jam’iyyar APC ta kasa, Ajibola Bashiru, da Hadiza Bala Usman za su rike mukaman Mataimakiyar Sakatare ta daya da ta biyu.
Sanarwar ta kara da cewa “Shugaban Majalisar Yakin Neman Zaben, Shugaba Tinubu, zai yi aiki tare da majalisar masu ba shi shawara da suka hada da Cif Bisi Akande, Cif Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha, Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Florence Ita Giwa.”
Sanarwar ta kuma kara da cewa “Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni an nada su a matsayin Mataimakan Darakta Janar na yakin neman zabe a Kudu da Arewa, inda su yi aiki tare da Sanata Bamidele Opeyemi da Sanata Jibril Barau a yankuna biyun.
“Sanata Adams Oshiomhole zai rike mukamin Mataimakin Darakta Janar mai kula da karfafa jama’a, yayin da Shugaban Ma’aikata zai rike mukamin Mataimakin Darakta Janar mai kula da Gudanarwa.
“James Abiodun Faleke, wanda ya taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaben 2022/2023, ya dawo a matsayin Mataimakin Darakta Janar mai kula da Tsare-tsare, Daidaito da Kulawa da Zabe.
“Faleke zai yi aiki tare da daraktocin yankuna, inda Sanata Olushola Adeyeye zai kasance na Kudu maso Yamma, Dr Ngozi Olejeme na Kudu maso Kudu, Sanata Uche Ekwunife na Kudu maso Gabas, Muntaqha Rabe na Arewa maso Yamma, Ahmed Muhammed Ketso Arewa ta Tsaka da Sanata Sani Danladi na Arewa maso Gabas.
“Ms Stella Okotete, Injiniya Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori za su kasance Sakatarorin Sashen Tsare-tsaren Zabe.
“Muiz Adeyemi Banire zai jagoranci Sashen Shari’a a matsayin Darakta, tare da Dr Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin mataimakansa. Sauran mambobin sun hada da Prince Lateef Fagbemi, tsohon Gwamna Ibrahim Shema, Worgu Boms da Dr Kingsley Tochukwu Udeh.
“Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris Malagi, zai rike mukamin Babban Daraktan Daidaita Sashen Yada Labarai da Sadarwa, tare da Dele Alake, Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu.
“Sashen Yada Labarai ya kuma hada da Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala da Felix Morka, wadanda aka nada a matsayin Mataimakan Daraktoci masu Daidaitawa.













































