Matashi ya mutu bayan ya fada kududdufi a jihar Kano

IMG 20260812 WA0110

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sanar da cewa wani matashi mai shekaru 18, Abdullahi Aminu, ya nutse tare da rasa ransa bayan ya fada wani kududdufi a Kofar Gabas da ke Karamar Hukumar Danbatta a Jihar Kano.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar Laraba a Kano.

Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata.

A cewar sanarwar, ofishin kashe gobara na jihar Kano ya sami kiran gaggawa daga Tashar Kashe Gobara ta Danbatta da misalin karfe 3:28 na yamma daga Aminu Lawan mahaifin mamacin, inda ya sanar da cewa dansa ya nutse a cikin kududdufin.

“Bayan samun rahoton, nan da nan muka tura jami’anmu na ceto zuwa wurin da abin ya faru,” in ji shi a cikin sanarwar.

Ya kara da cewa an ciro gawar matashin daga cikin kududdufin.

Jami’in hulda da jama’ar ya ce har yanzu ana ci gaba da binciken abin da ya janyo faruwar wannan hadari.

Ya ce daga baya an mika gawar mamacin ga Sakataren Hakimin Danbatta, Alhaji Baba Ado Sarkin Bai.

Abdullahi ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin, sannan ya yi kira ga mazauna yankin da su kiyaye yayin zirga-zirga a kusa da kududdufai da hanyoyin ruwa, musamman a lokacin damina. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here