Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Kiristoci da Musulmi a Najeriya da su daina zagin juna, inda ya bayyana cewa hakuri da juna tsakanin mabiya addinai daban-daban yana da muhimmanci domin zaman lafiya.
Sarkin ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a Abuja yayin Babban Taron Kasa da Kasa kan Tsaron Kasa domin Ciyar da Tattalin Arziki Gaba, wanda kungiyar Jama’atu Izalatil Bidiah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS Nigeria) ta shirya tare da hadin gwiwar Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League) ta kasar Saudiyya.
“Dole ne mu fada wa kanmu gaskiya cewa Kiristoci za su iya daina zagin Musulmi, Musulmi ma za su iya daina zagin Kiristoci. Kuma ta hakan ne za mu rayu cikin zaman lafiya,” in ji shi.
Ya bayyana cewa bai kamata Musulmi da Kiristoci su dauki kansu a matsayin wadanda suka fi juna ba, yana mai cewa dukkan mutane daidai suke a gurin Allah.
“Ba mu zo nan don mu ce mun fi kowa ba. Ba mu fi kowa ba. Allah ne ya halicce mu baki daya. Shi ne zai tantance wanda ya fi kyautatawa. Kuma ya san yadda zai yi hakan. Don haka ban zo nan don in ce na fi kowa ba,” in ji shi.
A karshen mako, Yahaya Jingir, wani malamin addinin Musulunci, ya bayyana cewa Kiristoci za su dauki kansu a matsayin wadanda suka fi Musulmi da a ce ba don takarar shugaban kasa ta Musulmi da Musulmi ba.
Sai dai Sarkin, wanda bai yi nuni kai tsaye ga kalaman Jingir a jawabinsa ba, ya ce babu wata kungiyar addini da ya kamata ta dauki kanta madaukakiya fiyye da wata.
“Ba mu zo nan don mu ce mun fi kowa ba. Ba mu fi kowa ba,” in ji shi.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su farfado da al’adar kula da makwabtansu, ba tare da la’akari da addininsu ko kabilar da suka fito ba.
“Allah ne ya halitta muku makwabtanku. Duk wanda ke makwabtaka da kai, ka san abin da ake bukata ka yi masa,” in ji shi.
Sarkin gargajiya ya nuna damuwa kan yadda ake yawan cin mutunci a shafukan sada zumunta, yana mai cewa wasu ‘yan Najeriya na yin karairayi da kalaman batanci ga shugabanninsu.
Ya ce mutanen da suka san suna yada karairayi game da shugabannin kasa, gwamnoni, sanatoci da sauran shugabanni, a karshe za su yi bayani a gaban Allah kan ayyukansu.
Sarkin ya bukaci ‘yan Najeriya da su mayar da hankali wajen magance matsalolin kasar maimakon fafutukar ganin ta tarwatse.
Ya bada misali da batun marigayi Abubakar Abdullahi, limamin da ya kare Kiristoci sama da 200 a cikin masallacinsa a jihar Plateau lokacin da ake cikin wani rikici, inda ya bayyana lamarin a matsayin misali na dabi’ar sanin darajar bil’adama da bai kamata a manta da ita ba.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar Hadin Gwiwar Addinai ta Najeriya (NIREC), Mista Cornelius Omonokhua, ya ce ba a halicci mutane a matsayin Musulmi ko Kiristoci ba, a matsayin ‘yan adam aka halicce su.
Omonokhua ya ce hukumar ta nuna ainihin ma’anar addini, wanda ya bayyana shi a matsayin juyayi da jin kai, inda ya kara da cewa hadin gwiwar da ke tsakanin shugabannin Kiristoci da na Musulmi ya nuna cewa addinan biyu ba sa yaki da juna.













































