Kasa ta 3 mafi kankanta a duniya ta sauya suna

Kasar Tsibirin Pacific na Nauru ta sanar da sunanta zuwa Jamhuriyar Naoero, kamar yadda Shugaban kasar, David Adeang, ya bayyana, inda yace sauyi yayi daidai da rubutu da furucin sunan a harshen kasa.

Lambar kasar ta duniya za ta canza daga NRU zuwa NRO, za kuma a dinga kiran mutanen kasar da dei-Naoero maimakon Nauruan.

Furucin da aka sani a kasashen waje da Now-roo, an maye gurbinsa, yanzu ana furtawa da Now-ero.

A cewar wata sanarwa da aka wallafa kwanan nan a shafin Facebook na gwamnati, wannan mataki zai dawo da wannan karamar kasar dake Kudancin Pacific zuwa sunanta na gargajiya.

Gwamnatin ta ce a baya sunan kasar ya zama Nauru a duniya kawai saboda sunanta na asali yana wahalar da ‘yan kasashen waje wajen furtawa, kuma hakan saboda samar da sauki ne, ba don so ba.

A watan Janairu, lokacin da shugaban kasar ya gabatar da wannan kuduru ga Majalisa, ya ce “Wannan sauyin da ake nema yana da nufin girmama gadon kasar mu, harshen mu da kuma asalin mu na gaskiya.”

A halin yanzu, majalisar dokokin kasar ta amince da gyaran kundin tsarin mulkin bayan zagayen kada kuri’u sau biyu kamar yadda doka ta tanada, amma har yanzu ba a bayyana ko an kammala gyaran takardar hukuma ba.

Kasar mai mutane 12,000, wadda ita ce kasa ta uku mafi karancin jama’a a duniya, bayan Tuvalu da Vatican City.

Wannan karamar tsibiri mai dutsen murjani ya taba kasancewa karkashin mulkin Jamus, daga baya kuma Ostiraliya ta rike shi kafin ta samu ‘yancin kai a matsayin jamhuriya a shekarar 1968.

Kasar ta fuskanci sauye-sauye da dama, inda hako phosphate ya samar mata wadata mai yawa a cikin shekarun 1970.
(AP/NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here