Gwamnan Kano ya yi ta’aziyya ga iyalin mawakin siyasa Kosan Waka

IMG 20260802 WA0277 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ta’aziyya bisa rasuwar fitaccen mawaqin siyasar Hausa, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, wanda ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 47 bayan wata gajeriyar jinya.

Wannan na kunshe ne cikin sakon ta’aziyya da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, iyalan sun ce za a binne mawaqin a garinsu na Tsanni, Karamar Hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina, da karfe 5 na yamma a ranar Lahadi.

Yusuf ya miqa sakon ta’aziyya ga iyalin marigayin, musamman ga mahaifiyarsa, da kuma abokansa, masoyansa da al’ummar Jihar Kano.

“Marigayi Kosan Waka jarumi ne na Kano dan asalin Katsina wanda wakokinsa sun wuce siyasa, ya zama wani jigo wajen inganta hadin kai, al’ada da wayar da kan jama’a,” in ji gwamnan.

Yusuf ya bayyana marigayin a matsayin daya daga cikin fitattun mawakan siyasa na Kano, wanda hazakarsa, kirkire-kirkire da kwarjinin da yake yi a wajen waka suka ba shi girma a fadin kasar.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Madaukaki Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, ya kuma yi fatan ya ba shi Aljannatul Firdausi, ya kuma baiwa iyalinsa hakurin jure wannan rashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here