‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukuma, sun kashe jami’an tsaro a Zamfara

Bandits 750x430

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Bungudu, a wani hari da suka kai cikin daren ranar Alhamis a gidansa, inda suka kashe jami’an tsaro hudu.

An rawaito ‘yan bindigan sun mamaye garin na Zango da ke da nisan kilomita 20 daga Gusau babban birnin jihar Zamfara cikin dare tare da kai wa gidan shugaban hari kai tsaye.
A yayin harin, ‘yan bindigar sunyi galaba kan jami’an tsaron da ke gadi, inda suka kashe ‘yan sanda biyu da ‘yan sa-kai biyu, sannan suka sace shugaban tare da wasu ‘yan uwansa.

Kokarin jami’an tsaro na fatattakar ‘yan bindigar ya gamu da cikas, saboda suna da karfin makamai, yayin da suka yi nasarar tafiya da shugaban.

SolaceBase ta rawaito daga cikin wadanda aka yi garkuwar akwai Hon. Nura Umar Abdullahi, Shugaban Karamar Hukumar Bungudu, Halliru Ahmad Soja wanda ma’aikaci ne a Asibitin Koyarwa na Tarayya Gusau da kuma Hussaini Naira mai POS da sayar da katin waya.

Wadanda aka kashe kuma sun hada da Inspector Basiru Lawal, Hamza Muhammad, Nura ADC da Ibrahim Ba’are.

Wani mazaunin garin ya ce harin ya kasance mai sauri kuma an tsara shi, imda ya ce jami’an tsaron sun nuna jajircewa, amma ba su iya ba saboda ‘yan bindigan sun fi su karfi.

“’Yan bindigan sun zo garin ne da niyyar yin abin da ya kawo su, jami’an tsaron shugaban sun yi iya kokarin amma an fi su karfi,” in ji shi.

Wannan shi ne sabon hari a cikin jerin hare-haren da ke ci gaba da faruwa a Zamfara duk da kokarin samar da tsaro da ake yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here