Mele Kyari ya magantu kan umarnin kamun da Majalisar Dattawa ta bayar a kan shi, ya musanta gujewa bincike

Kyari new GMD NNPC

Tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana shawarar da Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Asusun Jama’a ya dauka na fitar da takardar kama shi kan binciken da ake yi kan kudadin kamfanin a matsayin “na bammamaki”

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin, Kyari, ya bayyana cewa ya riga ya sanar da kwamitin cewa ba zai iya bayyana a gabansu ba saboda kulawar lafiyar da yake karba a kasar waje.

“A kan labarin takardar kamu da aka fitar a kan na a yayin zaman kwamitin ku mai daraja a yau, 10 ga Yunin 2026. Na firgita sosai kan fitar da takardar kamun,” in ji shi.

Tsohon shugaban Kamfanin ya ce ya sanar da kwamitin a hukumance ta hanyar wasika mai kwanan wata 11 ga Mayu na 2026, cewa yana karbar magani a wajen Najeriya.

A cewarsa, ya kuma bayyana shirinsa na amsa gayyatar kwamitin da zaran ya dawo kuma ya bayyana shirinsa na amsa kowace tambaya ta gaggawa ta hanyar lauyoyinsa.

“Haka kuma na bayyana shirin na amsa gayyatar Kwamitin da zaran na dawo Najeriya,” in ji shi. “Ina so in sake jaddada cewa a shirye na ke na amsa gayyatar Kwamitin na kuma bayyana a gabansa da zaran na dawo kasa.”

Tsohon shugaban NNPCL ya musanta zargin cewa ya yi watsi da gayyatar Majalisar Dattawa da gangan, yana mai cewa bai samu wata sabuwar gayyata ba kafin a fitar da takardar kamun.

Kyari ya bayyana cewa yanayin lafiyarsa a yanzu ya sa ba zai yiwu ya bayyana da kansa a gaban kwamitin ba, inda ya roki ‘yan majalisa da su tura duk wata tambaya ko neman karin bayani ta hanyar tawagar lauyoyinsa yayin da yake ci gaba da karbar magani a kasar waje.

Ya tabbatar wa kwamitin cewa zai ba da cikakken hadin kai ga binciken kuma ya yi alkawarin bayyana da kansa da zaran lafiya ta ba shi damar.

Da yake kare gwamnatinsa a kamfanin man fetur na kasa, Kyari ya ce tawagarsa ta sauya NNPCL daga kamfanin da ke yin asara zuwa kamfani mai samar da riba da ke tsaye da kafafunsa. Ya kara da cewa dukkan mu’amalolin da aka yi a lokacin mulkinsa an rubuta su yadda ya kamata kuma suna nan don idan ana bukatar dubawa.

Kwamitin na binciken kudadin da mu’amalar kamfanin mai, ciki har da batutuwan da suka shafi sama da Naira tiriliyan 210 tiriliyan ake bincike.

Sanata Victor Umeh ne ya gabatar da kudirin kamun kuma Sanata Adams Oshiomhole ya mara masa baya.

Sai dai Kyari ya dage cewa babu abin da yake boyewa kuma yana da kuduri na taimaka wa Majalisar Dattawa a binciken su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here