Masu yi wa kasa hidima 4 da soja 1 sun kone a hadarin mota a Adamawa 

IMG 20260603 WA0279 750x430

Wani mummunan hatari ya auku tsakanin motar sojoji da wata motar bas din fasinjoji kirar Hummer a kan babbar hanyar Girei–Song ta Jihar Adamawa, wanda yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, ciki har da masu yi wa kasa hidima hudu da soja daya.

Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru a ranar Laraba da misalin karfe 1:50 na rana, inda wuta ta tashi ta cinye motar bas din gaba daya, lamarin da ya haddasa mutuwar gaba daya fasinjojin da ke cikin ta.

Rahotanni sun ce motar sojojin ce ta fito daga Gombi zuwa Yola, yayin da bas din da ke dauke da fasinjoji 5 daga Yola zuwa Mubi, suka yi karo, bas din ta kife sannan ta fara ci da wuta nan take.

Da yake magana kan lamarin, mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Adamawa, Abdulrahman Tukur, ya ce: “Jami’an agajin gaggawa da na tsaro sun isa wurin da lamarin ya faru don ciro gawarwakin wadanda suka mutu da kuma tsaftace wurin da motar ta kone daga kan hanya.”

Shima mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce hatsarin ya faru ne a yankin Narehi da ke Karamar Hukumar Girei–Song.

Ya ce, “Abin bakin-ciki ne, dukkanin fasinjoji 5 da ke cikin bas din Hummer sun kone har lahira bayan motar ta kama da wuta sakamakon karo.

“Binciken farko ya nuna cewa 4 daga cikin wadanda suka mutu masu yi wa kasa hidima ne (NYSC) ne da aka tura su Jihar Adamawa.”

Ya bayyana sunayen biyu daga cikinsu Suleiman Juliet da Usman Shuaibu, duka ’yan asalin Jihar Kaduna ne, yayin da ake ci gaba da gano sauran wadanda suka mutu.

Nguroje ya kara da cewa wani soja da ke cikin motar sojojin ma ya rasu a hatsarin.

Ya ce jami’an ’yan sanda, tare da ma’aikatan agajin gaggawa, sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa, sannan an kai gawarwakin zuwa Asibitin Kwararru na Yola.

IMG 20260603 WA0294 768x1024

Ya ce ana ci gaba da kokarin gano ainihin wadanda suka mutu da kuma tuntubar iyalansu, tare da yin alkawarin ba da karin bayani yayin da bincike ke gudana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here