Kungiyar Malaman Kasa (NUT) ta umurci dukkan malamai a makarantun firamare da sakandare na gwamnati a Jihar Oyo su fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ga manema labarai a ranar Lahadi a Ibadan, ta ce wannan shawara ta samo asali ne saboda ci gaba da rike malamai da daliban da aka sace a jihar.
Wasu malamai da daliban makarantun firamare na Community Grammar School, Ahoro-Esinele, L.A. Primary School Ahoro-Esinele da Baptist Nursery and Primary School, Yawota, kusa da Ogbomoso, a karamar hukumar Oriire ta Jihar Oyo an sace su ne a ranar 15 ga Mayu.
Sanarwar da sakataren kungiyar, Mista Olukayode Salami, ya sanya wa hannu ta ce har yanzu ba a tabbatar da an ceto da sakin wadanda aka sace din ba cikin koshin lafiya ba.
Kungiyar ta ce ci gaba da tsare malamai da daliban ya haifar da tsoro da damuwa a tsakanin mambobinta, sannan yana hana iyaye aika ‘ya’yansu makaranta.
Kungiyar ta ce lamarin ya kara haifar da tashin hankali a garuruwan da abin ya shafa kuma ya haifar da damuwa kan tsaron malamai da masu koyo.
Ta ce yajin aikin yana nufin jan hankalin hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki kan bukata a gaggauta da kara kaimi don tabbatar da sakin wadanda aka sace.
Kungiyar ta umurci dukkan malamai a makarantun firamare da sakandare na gwamnati a jihar da su daina zuwa aiki a makarantu daga ranar 1 ga Yuni har sai an sake fitar da wata sanarwar.
NUT ta bukaci mambobinta su bi umurnin gaba su kasance masu biyayya ga doka kuma su zauna lafiya a gidajensu a duk tsawon lokacin yajin aikin.
Kungiyar ta kuma jaddada goyon bayanta ga malamai, daliban da aka sace da iyalansu, tana mai tabbatar musu da ci gaba da basu goyon bayanta.
Ta kara da cewa za ta ci gaba da tattaunawa ta hanyoyin da suka dace da hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki har sai an samu ‘yantar da wadanda aka sace.
NUT ta sake jaddada aniyar ta na tabbatar da jin dadi, tsaro da lafiyar malamai da masu dalibai a fadin kasa. (NAN)












































