Shugaba Bola Tinubu ya iso Legas a ranar Juma’a bayan kammala ziyar kasashe uku zuwa Faransa, Kenya da Ruwanda, wacce nufinta shi ne jawo hankali masu zuba jari da kuma daidaita Najeriya domin samun ci gaban tattalin arziki.
Jirgin shugaban ya sauka da karfe 7:12 na yamma a Sashen Shugaban Kasa na Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, Legas.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, Mataimakin Gwamna Femi Hamzat, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Kasa Femi Gbajabiamila da sauran jami’an gwamnati ne suka tarbi Tinubu a filin jirgin.
Haka kuma, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, tare da sauran manyan masu rike da mukaman siyasa da jami’an gwamnati sun kasance a filin jirgin.












































