Tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC, yana mai danganta hakan da mummunan yanayin siyasa, rikice-rikicen cikin gida, da abin da ya bayyana a matsayin katsalandan daga waje da ke kawo cikas ga zaman lafiyar jam’iyyar.
A wani sako da ya wallafa a shafin X ranar Lahadi, Obi ya ce matakin da ya dauka ba saboda wata matsala ta kashin kansa da shugabannin jam’iyyar ba ne, sai dai saboda yawaitar rarrabuwar kai, zato, da tarwatsa tsari da ya sa yin aikin gina kasa na gaskiya ya yi wuya.
“Ina so na bayyana karara, matakin da na dauka na ficewa daga ADC ba saboda shugabanmu mai girma, Sanata David Mark, ya yi mini mummunan abu ba, ko kuma shugabana kuma babban yayana, Alhaji Atiku Abubakar, ko wani daga cikin manyan shugabanni sun yi mini wani abu mara kyau ba,” in ji Obi. “Zan ci gaba da girmama su.”
Yayin da yake kokarin yin hidima cikin gaskiya a ƙarƙashin mawuyacin yanayi.
“Akwai lokutan da nake tambayar Allah a addu’a: Me yasa yin abin da ya dace ake yawan ganinsa a matsayin laifi a kasarmu?” in ji shi. “Me yasa ba a daraja gaskiya?”
Ya kammala da sake tabbatar da imaninsa kan makomar Najeriya duk da kalubalen.
“Duk da komai, na kasance mai jajircewa. Na yi imani kwarai cewa Najeriya za ta iya zama kasa mai shugabanci nagari da ya ginu kan adalci, tausayi, da damar da ta dace ga kowa,” in ji Obi. “Sabuwar Najeriya mai yiwuwa ce.”












































